Dole Mu Daura Damara Don Samun Nasara A Zaben 2023 - ROCHAS

Tsohon Gwamnan jihar Imo kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa, Rochas Okorocha.

Yayin da jamiyyar APC ke shirin gudanar da taron fidda da wanda zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a zaben kasar da ke tafe a shekarar 2023, Tsohon Gwamnan jihar Imo kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar ta APC.

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa dole jam’iyyar APC ta sake daura damara don samun nasara a zaben shugaban kasa da ke tafe nan da yan’watanni, a cewarsa akwai matsaloli da yawa da ke gaba musamman kafin ranar zaben fidda da gwani na jam’iyyar,

Batun inda za’a kai shugabancin kasar daga jam’iyyar da kuma rahin sanin tabbas na wanda shugaba Muhammadu Buhari ke so ya tsayawa jam’iyyar takara wajen maye gurbinsa na daga

Cikin matsalolin dake gaban jam’iyyar a cewar Rochas ga kuma Gwamnoni da su ma ke wani gefen da kuma uwa- uba wakilan jam’iyyar da ke jiran ranar zaben na fidda gwanin ya karaso.

Kan batun ko yana daga cikin wadanda za su amince idan shugaban Buhari ya bukaci duk wani dan takara ya janye a marawa mutum daya baya ba tare da an yi zabe ba,

Rochas ya ce ’ya danganta da yanda aka yi maganar idan aka ce Rochas bai kamata ka tsaya takara ba sai abani dalili, ba’a sa mutane dole wai sai ka sauka’’

Ya na mai kari da cewa sai kowa ya yarda, don yana iya yiwa wani ya yarda wani bai yarda ba kuma idan aka samu hakan to dole sai an yi zabe .

APC

A gefe guda Shugaban kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC John Odigie Oyegun ya ce duk ‘yan takara a yanzu sun amince da fidda dan takara ta hanyar daidaitawa sai daya tak ne daga cikin su ya ki amincewa.

Oyegun na nuna cikin ‘yan takara 23, 22 sun amince da za su janye don samun dan takara ta hanyar daidaitawa, amma daya daga ciki bai amince ba ya na mai bukatar a gudanar da zabe ko kuma sai in shi ne za a tsayar.

Oyegun ya nuna don bukatar jam’iyyar ta samun wanda zai gaji shugaba Buhari daga cikin su, sai sun rage yawan ‘yan takarar duk da kowannen su ya lashe matakin farko na tantancewar.

Jita-jita ta yi yawa inda a ke nuna wanda bai amince din ba shi ne Bola Tinubu.

An dai ware ranar 6 da 7 na watan yuni nan domin gudanar da zaben fidda da gwanin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC sa Abuja inda ‘yan takara 13 za su fafata biyo bayan watsi da mutum 10 da kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar ya yi.

Saurari Hirar da shamsiyya Hamza Ibrahim ta yi da Rochas

Your browser doesn’t support HTML5

Dole Mu Daura Damara Don Samun Nasara A Zaben 2023 - ROCHAS