Jam’iyyar All Porgressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya, ta soke sunayen ‘yan takara 10 daga cikin 23 da ke neman tikitin tsayawa jam’iyyar takara a zaben shugaban kasa da za a yi badi.
Shugaban kwamitin tantance ‘yan takara da jam’iyyar ta kafa, John Oyegun ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.
Jam’iyyar ta APC ta fara aikin tantance ‘yan takarta a ranar Litinin din da ta gabata, ta kuma kammala a ranar Talata.
Bayanan soke takarar mutanen, na zuwa ne yayin da kwamitin ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Oyegun ya ki ba da sunayen wadanda aka soke takararsu a lokacin da aka tambaye shi.
Hakan na nufin a tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan nan na Yuni, APC za ta yi zaben fitar da gwani da ‘yan takara 13 da ke muradin ganin sun gaji Shugaba Muhammadu Buhari, wanda wa’adin mulkinsa na biyu zai kare badi.
Kadan daga cikin wadanda suke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar wacce ta kwashe shekara bakwai tana mulki, akwai mataimakin shugaban kasa mai ci Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan.
Sauran sun hada da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar da sauransu.
Tun a makon da ya gabata babbar jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party (PDP) ta fitar da dan takararta, inda ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.