Dokar ta Baci: Ana Takaddama a Majalisar Dattawa

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.

Ana nan ana tafka muhawara a Majalisar Dattawan Nijeriya kan bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta sake kafa dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. A gobe ake sa ran su ma 'yan Majalisar Wakilai za su shiga tattaunawa a kai.

Bukatar Shugaban Nijeriya ta sake kafa dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya mai fama da rigingimu na gamuwa da turjiya a Majalisar Dattawan Nijeriya.

Wakiliyar Sashin Hausa Madina Dauda ta ce an yi ta muhawara da takaddama da rigingimu kan wannan bukatar har ta kai ga sai da aka bukaci ‘yan jarida su fice. Madina ta ce bayan mahawarar ta cikin sirri sai Shugaban Majalisar Dattawa David Mark ya gaya ma ‘yan jarida cewa yau Laraba za a cigaba da tattaunawa.

Da Madina ta tuntubi Sanata Sahabi Ya’u, sai ya nuna goyon bayansa ga bukatar sake kafa dokar ta bacin da cewa idan ba a yi hakan ba, babu madadin hakan na hakika. To amma ya ce lallai akwai daure kai ganin yadda aka yi ta kafa dokar a baya ba tare da wani cigaba ba. Saidai da ta tuntubi wani tsohon Dan Majalisar Wakilai daga jihar ta Borno, Dr. Haruna Yarima sai ya nuna rashin amincewarsa da sake kafa dokar saboda rashin tasirin dokar a baya.

Shi kuwa wani dan jam’iyyar adawa ta APC, Injiniya Khailani Muhammad ya yi zargin cewa yinkurin sake kafa dokar na da nasaba da take-taken Shugaban Goodluck Jonathan na ganin ba a yi zabe a yankin ba, sannan ya yi tir da halayyar ‘yan arewacin Nijeriya da ke Majalisun Dattawa da Wakilai, wadanda ya ce duk da rinjayensu ba su amfanar arewacin Nijeriya sosai.

Madina ta ce shi kuwa Kakakin Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal y aba da umurnin katse hutun ‘yan Majalisar don a tattauna kan wannan bukatar a gobe alhamis.

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar ta Baci: Ana Takaddama a Majalisar Dattawa