Jigajigai a Majalisar Dattawan Amurka sun yanke shawarar cewa sai 'yan Republican sun samu kuri'u 60 kafin su iya barin tanajin hana zubar da ciki a sabon kudurin dokar maye dokar saukaka jinya ta 'Affordable Act,' wadda ake kuma kira Obamacare.
'Yan Republican na da rinjayen 52 akasin 48 a Majalisar. Da matukar wuya 'yan Democrats su kada kuri'ar goyon bayan kudurin dokar da za ta hana mata zubar da ciki.
Haka zalika, da matukar wuya ace wasu 'yan Republican su goyi bayan kudurin dokar ba tare da tanajin hana zubar da ciki ba.
Sanata Bernie Sanders dan Democrat ya aika da sako ta twitter mai cewa, "Shawarar da jigajigan Majalisar su ka yanke yau na sake tabbatar da cewa tsarin da 'yn Republican su ka bullo da shi na soke Obamacare shirme ne.
To amma 'yan Republican sun ce shawarar ta jigajigan Majalisar shawara ce kawai, don haka ana iya canza ta.