Sai dai wasu na ganin haka ta kusa ta cimma ruwa ganin cewa wannan gwamnati ta dukufa wajen ganin an yi nasarar samar da sauye-sauyen.
Hakan kuma na faruwa ne yayin da ‘yan majalisar dokokin wakilai ta ce ta kammala aiki kan dokar wacce aka fi sani da PIB a takaice.
“Saboda mahimmancin wannan doka ne ya sa majalisa ba ta yi gaggawar yin wannan doka ba, saboda an taba samun kuskure a wata majalisa a baya can, kan tsarin nan na tono mai a cikin teku da kuma doron kasa, amma yanzu a nan majalisar wakilai mun riga mun aika da shi.” In ji Muhammed.
Dangane da inda aka kwana kan wannan doka a majalisar dattawa, wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda, ta tambayi Sanata Kabiru Gaya, wanda ya ce mata akwai batutuwa da dama da ake so a duba.
“Muna so mu tabbatar cewa yadda ake daukan man har yanzu ba mu gamsu ba, an ce kai me sayen man kai za ka zo da jirginka da mita ka diba ka kuma fadi yadda ka diba, to ya zanzo na diba kaya na biya, duk gaskiya ta wata rana a sai na yi rashin gaskiya.” In ji Sanata Gaya.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5