A makon jiya ne gwamnatin jihar Lagos ta kafa dokar data tanadi cewa duk mai son yin karatu a makarantun jihar to dole ne ya iya harshen Yarbanci. Dr. Yomi Layinka kakakin gwamnatin jihar Oyo yace, a jiharsu abin da suke bukata shine mutum ya iya akalla daya daga cikin manyan yaren Najeriya, wato Hausa, Igbo ko Yarbanci.
Shi ko Mr. Olabisi wani mahaifi ne da yace dokar da Lagos ta yi zata sa mutane su san yarensu da al'adunsu. Wani Olagunju wanda malamin makaranta ne yace yayi maraba da dokar. Hakan zai taimaki dalibai su san yarensu. Malam Mukaila Agunbiade cewa yayi bai kamata gwamnatin Lagos ta tsayar da dokar ba, saboda ba Yarbanci kadai ne yaren Lagos ba.
Yace akwai yare iri-iri a jihar. Kamata yayi ya samar da masu koyar da Yarbancin domin a iya, inji Agunbiade. Lauya Abiodun Abdulrahim yace dokar jiharsu ce, duk abinda suka ce ta zauna. Dole ne duk wanda yake son ya shiga babbar makarantar jihar ya koyi yaren. Amma bai goyi bayan gwamnatin jihar ba kuma yace gwamnatin tarayyar Najeriya na iya kalubalantar dokar a kotu.
Wani dalibi ma cewa yayi dokar bata dace ba musamman ga dalibi mai karatun kimiyya ace sai yayi harshen Yarbanci. Kamar yadda Muryar Amurka ta gano jihohin Oyo, Osun, Ogun da Ondo basu dau wani matsayi ba akan dokar ta Lagos.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal don karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5