Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2019: Mutanen Jihar Imo Sun Kalubalanci Zabin Gwamna Okorocha


Gwamnan Imo Rochas Okorocha
Gwamnan Imo Rochas Okorocha

Bisa furucin wasu 'yan jihar Imo da wuya hakar gwamnan Rochas Okorocha ta cimma ruwa na ganin cewa sirikinsa ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar shekara mai zuwa.

'Yan asalin jihar Imo sun ce sam ba za ta sabu ba bayan da gwamnansu Rochas Okorocha ke kokarin ya nada sirikinsa, a matsayin wanda zai gaje shi a shekarar 2019..

A farkon wannan makon ne gwamnan ya fito fili ya ce ya na son sirikinsa Uche Nwosu, wanda yanzu yake auren babbar diyarsa, ya gajeshi a matsayin dan takarar da zai nemi kujerar gwamna.

Mr. Ugochukwu Ubum, wanda Muryar Amurka ta zanta da shi ya ce gwamnan ba ya wani abin a zo a gani a jihar saboda haka "gara da shi da sirikin nasa su tafi wani sabo ya kama mulkin jihar."

Ana ta bayanin, Sandra Godwin, ta ce bai dace ba sirikinsa ya gaje shi ba. domin a nata tunanin duk umurnin da Rochas ya bashi ne zai bi.

Wani Mr. Ibe Johnson ya ce hakan na nuna cewa ya na matukar son sirikinsa amma duk yadda aka dubi lamarin a gane cewa ba'a kirkiro jihar domin Rochas da iyalinsa kadai ba.

"Yunkurin nashi ba wani abu ba ne illa matukar son kai"Inji Johnson.

A saurari rahoton Alphonsus domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG