A baya dai kafin soma amfani da kafofin sadarwa na internet, sana’ar sayar da jarida, sana’a ce da akan yi rububin shiga.
Sai dai da alamun ba haka lamarin yake ba a yanzu, inda, masu sana’ar sayar da jaridun ke kokawa game da rashin kasuwa musamman a wannan lokaci.
Malam Ali Muhammad wani dattijo ne da ya shafe fiye da shekaru 30 da uku yana sana’ar sayar da jarida a Najeriya,ya ce, yanzu sun zama yan kallo,biyo bayan bullowar harkar jarida ta kafar sadarwa, wato internet.
Malam Adamu Idris, tsohon mai sai da jarida ne a Yola, jihar Adamawa, ya ce yanzu babu batun yan free-readers,tun da yawancin jama’a na da wayar salula.
Free-readers, su e mutane da suke ba da dan wani kudi su samu damar karanta jarida a wajen masu sayar wa.
Su ma dai masana harkar jarida da yada labarai na danganta lamarin da koma baya ga harkar karance-karance da ake da shi a yanzu, baya ga rashin kudi da kuma wayar salula da yanar gizo da zamani ya zo da su.
Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani kan wannan rahoto.
Facebook Forum