Masharhanta harkokin siyasa da yawa na kallon zaben Amurka a matsayin mai zafi, amma Dr. Salihu Muhammad Niwuro, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar IBB Lapai da ke jihar Neja a Nigeria, ya ce akwai darasin da kasashen Afrika ya kamata su dauka a zaben na Amurka.
Abu na farko a harkar zaben Shugaban kasa na Amurka, a cewarsa, shine jama'a su duba abinda zai amfani kasashensu da 'yan kasarsu musamman ta bangaren dangatakar diflomasiyya da manufofin kasa-da-kasa.
Sai dai ra'ayi ya bambanta a tsakanin 'yan Nigeria akan wanda suke goyon baya tsakanin manyan 'yan takarar Amurka biyu, Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da tsohon mataimakin Shugaban kasa Joe Biden na jam'iyyar Democrat.
Alhaji Yahaya Danladi Musa, mazaunin garin Lokoja ne a jihar Kogi, ya yi fatan alheri ga Amurka a zaben ko da ya ke ya bayyana goyon bayansa ga jam'iyyar Democrat saboda a cewarsa, wani jawabi da Biden ya yi ya ce zai kare tsarin kiwon lafiyar Obamacare ya kuma kara inganta shi ta yadda Amurkawa zasu kara samun sauki. Bayan haka zai inganta dangantakar Amurka da kasashen duniya.
Shi kuwa Malam Mansur da ke zama a garin Minna a jihar Neja, cewa ya yi idan aka yi la'akari da ayyukan da Trump ya yi za a ga cewa tun da ya hau mulki babu wata kasa da Amurka ta kai yaki a karkashin gwamnatinsa, ba kamar wasu gwamnatocin kasar da suka shude ba.
Yanzu dai kallo ya koma Amurka a wannan makon don masu iya magana na cewa "ba a san maci tuwo ba sai Miya ta kare."
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5