Deborah Samuel Ta Shiga Jerin Sunayen Wadanda Aka Kashe Sabili Da Addininsu

Deborah Samuel

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta karrama Deborah Samuel dalibar da ta gamu da ajalinta a kwalijin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a hannun wadansu masu tsattsauran ra’ayi.

Labarin kashe Deborah ya karrada kafofin sada zumunta bayan da aka nuna bidiyon yadda aka kashe dalibar da ke shekara ta biyu a kwalejin, wani amari da ya dauki hankalin jama’a da dama a ciki da wajen Najeriya.

A sanarwar da ma’aikatar da wallafa a shafin ofishin da ke sa ido kan kare ‘yancin addini na internet, a ranar tunawa da wadanda aka kuntatawa sabili da addininsu, an kafa hoton Deborah a shafin farko kamar yadda cibiyar ta saba yi domin haska fitila da jan hankali kan rayuwar wadanda su ka fukanci kuncin rayuwa sibili da addininsu, da labarin su ya dauki hankali a kasashen duniya.

Deborah Samuel

A bayanin da aka wallafa a shafin karkashin hoton Deborah, ofishin ya bayyana cewa, “A watan Mayu, wadansu gungun mahara suka yi ta jifar da duka, daga nan suka cinnawa dalibar kwaleji Deborah Samuel a Najeriiya su ka kashe ta, a wani hari da kiyayya da zargin batanci ya haifar, duk da cewa hukumomi sun yi kokarin hana wa. Muna karrama rayuwar ta, yayin da mu ke ci gaba da aiki domin kawo karshen irin wannan mugun tashin hankalin”

Daborah Samuel ita ce ta baya bayan nan da ofishin ya haska fitila a kai, a shafin sa na internet.

Wadanda ofishin ya karrama a baya sun hada da wani mai bin addinin Buda Nguyen Bac Truyen wanda hukumomin kasar Vietnam suka gasawa akuba suka yanke mashi hukumcin daurin shekaru goma sha daya a gidan yari a shekara ta 2017 sabili da addinin da ya zaba, lamarin da ya yi sanadin rashin lafiyar da ya yi fama da shi.

Ofishin 'Yancin Addini na duniya yana karfafa muhimmancin mutunta yancin addini, ko imani, ga kowa. Yana kuma sa ido kan cin zarafin bil’adama, da wariya da suka shafi addini a duk fadin duniya. Ofishin yana kuma ba da shawarwari da su ka jibinci ‘yancin addini, da karfafa aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin dakile aukuwar matsalolin da su ka shafi take ‘yancin addini ga kowanne bil’adama da ke haifar da tashin hankali.

Ku Duba Wannan Ma Daliba Ta Rasa Ranta A Sokoto Bayan Da Aka Zarge Ta Da Yin Sabo