Kungiyar Kiristoci ta CAN a Najeriya ta yi kira ga daukacin mabiyanta a fadin kasar da su fito don yin tattaki na musamman don nuna rashin jin dadinsu da irin kisa da aka yi wa wata budurwa, Deborah Samuel a kwalejin ilimi na Shehu Shagari a jihar Sokoto.
Kungiyar a wata sanarwa da ke da sanya hannun sakatarenta, Joseph Daramola, ta kuma bukaci masu tattakin su rike sakonni da zai nuna neman adalci ga Deborah.
Shugaban kungiyar CAN a jihar Nasarawa, Very Rabaran Sunday Emah ya ce sun ji takaicin kisan Deborah Samuel don haka suka bukaci mabilya addinin kirista da su gudanar da addu’o’i da koyarwar zaman lafiya a majami’unsu.
Shugaban kungiyar ta CAN a jihar Filato, Rabaran Fada Polycarp Lubo, ya ce za su gudanar da sujada da addu’o’i na musamman ne a ofishin kungiyar CAN.
Tun farko gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a wani taro da ya yi da shugabannin addinai a jahar, ya bukace su ne su ja hankalin magoya bayansu, don kaucewa tashin hankali.
A yammacin ranar Lahadi ne Kirista a fadin Najeriya za su gudanar da addu’o’in a wuraren da suka kebe.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: