Babu wani tabbacin bayani a yanzu da ke nuna tsohon shugaba Jonathan yana son amshe madafun jam’iyyar, don shirya babban taron zaben sabbin shugabanni da zai kawo karshen rabewar jam’iyyar gida biyu.
Abin da ya fito fili shine mara bayan Jonathan da hukuncin da kotun ‘daukaka ‘kara ta zartar, wanda ya baiwa Sanata Sheriff shugabancin jam’iyyar da kuma soke aikin kwamitin riko na Ahmad Makarfi.
Tsohon Minista a ma’aikatar kudi Yerima Lawal Ingama, yace manyan jam’iyyar zasu taru don baiwa Sheriff shawarar yadda zai dinke barakar jam’iyyar yana mai nuna amanna ga jagorancin Sheriff zai kai jam’iyyar ga samun nasara.
Sheriff wanda ya gana da tsohon shugaba Jonathan, yace yana tuntubar sauran iyayen jam’iyyar don neman shawara. Kuma yace sauran shugabannin jam’iyyar suna son ayi mata gyara idan aka dauke masu son rai.
Wasu gwamnonin PDP irin su Ayo Fayose, na cewa sam ba zasu tafi da Sheriff ba wanda hakan ne ma ya sanya karfin yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyyar PDP wadda ake kira APDP wato Advance People Democratic Party.
Sai dai ba mamaki bayan wannan ganawa da za ayi za a fahimci inda alkiblar PDP ta dosa, daga haduwar dattawan jam’iyyar da zasu bayyana a taron sulhun.
Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5