Ana kuma bukatar yin allurar rigakafi don dakile cutar a Zabarmari da babban birnin jihar Maiduguri.
"Muna cikin tattaunawa da hukumomi kuma muna shirin tallafa musu a wani kamfen na riga-kafi da za a fara a Maiduguri da Zabarmari da zarar an samu allurar riga-kafin, saboda kyanda na da saurin yaduwa kuma tana da mummunar hadari musamman ga yara kanana," in ji David Thérond, MSF shugaban mishan din.
Har yanzu dai tattaunawar game da shirin riga-kafin na karkashin matakan jihohi da na tarayya tare da ma na Ma’aikatar Lafiya da Hukumar Lafiya ta Duniya.
MSF na kula da yara da suke fama da cutar kyanda a asibitin yara na Gwange da ke Maiduguri.
An kwantar da yaro na farko a ranar 3 ga watan Disamba, kuma adadin marasa lafiya ya karu tun daga lokacin a asibitin Gwange da ma sauran asibitocin Maiduguri.
Daga 1 ga Janairu zuwa 3 ga Afrilu, MSF ta kwantar da yara 1,158 da ke fama da cutar kyanda a asibitin yara na Gwange, wanda kashi 58 cikin ɗari suka fito daga Zabarmari, da ke da nisan mil 12 daga Maiduguri.