Daruruwan Matafiya Sun Makale A Hanya Saboda Boren Masu Manyan Motoci A Neja

Yadda masu manyan motoci suka danse hanya a Neja

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce babu ja da baya akan rufe hanyar Minna zuwa Bidda har sai an kammala gyaran a cewar Kwamishinan Ayyuka Alh. Mammam Musa.

Daruruwan matafiya sun shiga wani hali na tsaka mai wuya a sakamakan rufe hanyar motar Suleja zuwa Minna da kuma hanyar Bidda zuwa Mokwa da direbobin manyan motoci suka yi a jihar Neja.

Masu manyan motocin sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda Gwamnatin jihar Nejan ta rufe hanyar Minna zuwa Bidda ga masu manyan motocin, hanyar da ta rage da kyau da ta hada Arewacin Nigeria da kuma kudancin kasar,

Kwamred Faruk Kawo jigo ne a kungiyar Direbobin Tanka a Najeriya ya ce bakar wahalar da suke sha ne ya sa su dauki wannan mataki.

“Idan ka dauka daga Bidda zuwa Lambatta ba hanya, motoci sun fadi abin ya cushe.” In ji Kawo.

Yadda matafiya suka tsaya dako-dako a hanyar Neja bayan da masu manyan motyoci suka rufe hanya

Alh.Umma Kolo shi ne Mai baiwa Gwamnan jihar Neja Shawara akan Harkokin siyasa ya ce akwai bukatar Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin yara manyan hanyoyin da suka ratsa ta jihar ta Nejan.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce babu ja da baya akan rufe hanyar Minna zuwa Bidda har sai an kammala gyaran a cewar Kwamishinan Ayyuka na jihar Nejan Alh. Mammam Musa.

“Mu matsayinmu shi ne bai yi wa mu bude hanya saboda hanyar bai biyiwa don ana aiki saboda ba kananan kudi aka zuba ba don a yi wannan ayyuka ba. Manyan motoci suna bata aikin.”

A yanzu dubban motoci ne suka cika garuruwan Lambatta da kuma Bidda a sakamakon datse hanyoyin da masu manyan motocin suka yi.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Daruruwan Matafiya Sun Makale A Hanya Saboda Boren Masu Manyan Motoci A Neja - 2'50"