Haka zalika Gwamnatin jihar Nejan ta ce masu hawa babura a duk fadin Jihar musamman ‘yan achaba za su fara aiki daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma.
Gwamnatin Nejan dai ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda kokarin shawo kan matsalar rashin tasaro da ya addabi jihar kamar yadda sakataren Gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane ya ce.
"Gwamnan jihar ta fito ne da wasu sabbin matakan tsaro abin da zai kara ba da zaman lafiya."
Malam Jibrin Muhammad wani mazaunin karamar hukumar Shiroro da ke fama da matsalar ‘yan bindiga ya ce sun yi maraba da wannan mataki na gwamnatin jihar.
A yanzu dai jihar Nejan tabi sahun jihohin Zamfara da Kaduna wajen daukar irin wadannan matakai da ake fatan zai taimaka wajen shawo kan mtasalar ‘yan bindiga.
Mafi akasarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya, na fama da matsalar 'yan fashin daji da ke sace mutane don neman kudin fansa.
'Ya bindigar kai kai hare-hare a kauyuka da garuruwa tamarin da ke kai ga asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: