Dangote Da Bill Gates Zasu Yaki Tamowa

A yau alhamis ne mujajjalar Vanguard ta wallafa cewar hamshakin dan kasuwan nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka malam Aliko Dangote, da attajirin nan na kasar Amurka mai kanfanin kera wasu manhajojin na'ura mai kwakwalwa Mr Bill Gate, sun cimma wata matsaya akan yaki da tamowa wadda rashin abinci mai gina jiki ke haifarwa wa musamman ga kananan yara a Nahiyar Afirka.

Manyan attajiran sun bada sanarwar wani shiri na samar da kudi dalar Amurka miliyan dari domin kafa gidauniyar da zata yaki da tamowa wadda rashin isashshen abinci maigina jiki ke haifarwa ga yara matasa a nahiyar Afirka.

Malam Aliko Dangote wanda asalin dan Najeriya ne ya bayyana cewar hada hannu da gidauniyar sa mai suna Dangote Foundation ta yi da ta attajirin dan kasuwa Bill Gates mai suna Melinda Gates, zai magance matsalar rashin abinci mai gida jiki wanda ta addabi kananan yara kusan miliyan 11 a arewacin Najeriya.