An sabunta shafin Facebook cikin sabuwar manhajjar kwamfuta ta Window 10, wadda kamfanin Microsoft ya fitar, inda aka kara mata saurin sarrafa ayyukanta cikin sauki.
Haka kuma an bukasa shafin Facebook da wasu hanyoyi na zamani da baza su iya aiki da tsofaffin manhajojin da ake dasu a baya, hanyoyin sun hada da yadda mutane zasu iya rarraba hotuna da abinda suka rubuta da hotunan bidiyo ga abokansu cikin sauki da sauri.
Masu ita wannan manhajja ta window 10, zasu iya ganin wannan cigaba da aka samu karara, kamar yadda tsarin ajiye bayanan abokai da yadda ake fitar da sanarwa da dai sauransu.
Haka zalika duk masu amfani da wannan manhaja zasu iya gane wanne abokansu ne keda wannan sabuwar manhajja, kai hatta kalandar da take wannan manhajja ta fita daban.
Yanzu haka dai mutane biliyan 1.44 ne ke amfani shafin Facebook a wata, acewar wata sabuwar kididdiga da ta fito cikin wannan shekara, kididdigar dai ta nuna karuwa da koso 13 cikin 100 na yawan mutanen da ke hawa duk wata a shekarar da ta gabata.