Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamu Tsoron Super Eagles, Tunisiya Ba Nijer Bace Inji Koc Missaoui


Kocin kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Tunisiya Hatem Missaoui ya ce ‘yan wasan shi basa shakka ko tsoron ‘yan wasan Najeriya a karawar da zasu yi da Najeriyar na ‘yan rukunin C a gobe juma’a.

Kungiyoyin biyu zasu taka ledar ne a filin wasan Kigali a karawar farko ta wassanin da za’a buga a ranar.

‘Yan arewacin nahiyar Afirkan sun fara Kanfe tun a lokacin da aka buga wasanin cin kofin nahiyar Afirka yayin da suka yi kunnen doki da Guinea inda wasan ya tashi da ci 2-2.

Kungiyar super Eagles kuma ta lallasa Niger da ci 4-1, koc din ya kara da cewa koda shike ana girmama ‘yan wasan super Eagles amma hakan bazai razana suba.

Missaoui ya fadawa manema labarai a Kigali cewa “baza su taba jin tsoron ‘yan wasan super Eagles ba, ya ce idan har suna jin shakkar su to ba anfanin tunkarar su a fagen wasa,” Koc din ya kara da cewa ‘yan wasan super Eagles sun taka rawar gani a karawar su da Nijer, amma Tunisiya ma nada fitattaun ‘yan wasa.

Koc din ya ce Wasan zai yi armashi sosai, kuma suna ba Najeriya girma amma suna da tawagar da zata iya doke tawagar Najeriya, daga karshe Missaoui ya ce Super Eagles ta lallasa Nijer amma ba dai Tunisiya ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG