Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Pillars Zata Samu Hamshakin Dan-Wasa Chikatara


Tambarin Kano Pillars
Tambarin Kano Pillars

Tsohon dan wasan zakaru na kungiyar kwallon kafar Najeriya, Chison Chikatara, ya bayyanar da aniyar shi ta rattaba hannu a kan kwantiragi na wasu shekaru da kungiyar kwallon kafar Kano Fillars a kakar wasa mai zuwa.

Shi dai dan wasan dan asalin jihar Abia ne kuma mai tsaron gida na kungiyar Super Eagles ne, ya dai yi suna a wasan da suka gwabza da ‘yan wasan kasar Nijar inda aka tashi da ci 4 – 1 a ranar litinin, a wasan farko na gasar cin kofin zakaru na kasashen Afrika.

Shi dai dan wasan Chikatara yayi rawar gani inda ya sama ma kungiyar tasu maki 3, hakan dai yasa anata maganar yadda zai iya zama a nan gaba.

Har ya zuwa yanzu bamu saka hannu da dan wasa Chikatara ba, amma muna sa ran zamu cinma matsaya, tun da ya gaya cewar kungiyar Kano Pillars itace kungiya da yake so ya buga ma wasa a kaka mai zuwa.

A dai tabakin mai magana da yawun kugiyar ta Kano Pillars Idris Malikawa, yace dan wasan Chikatara ya same su kuma ya nuna musu cewar zai so ya buga musu wasa idan zasu so hakan.

Shi dai dan wasan chikatara ana kiran shi da suna dan-giginya “Kolanut Boy” a turance, ya kuma bugama wata kungiya a kasar Switzerland a shekara da ta gabata, kamin ya dawo kungiyar Abia Worriors, amma basu bashi wata kwantiraki mai tsoka ba wanda hakan yasa zai bar su zuwa Kano Pillars.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG