Ga dukkan alama kamfanin sada zumunta na Meta wanda aka fi sani da Facebook ya cire shafin fitaccen mawakin nan dan arewacin Najeriya mai suna Dauda Kahutu Rarara daga dandalin, bayan da mabiyan mawakin suka kai wa kamfanin korafi.
Matakin cire shafin dai na zuwa ne bayan da Rarara ya wallafa wata waka ta yabon shugaban Najeriya Bola Tinubu saboda yadda yake magance matsalolin talauci da tsaro a Najeriya.
A ranar Asabar ne dai aka cire shafin sada zumuntar mawakin na Facebook, wanda ke da mabiya sama da miliyan daya. Wakar da mawakin ya yi ta yaba wa Tinubu kan yadda ya ke kawar da yunwa da rashin tsaro a Arewacin kasar, a cewarsa “yanzu ‘yan Arewa sun yi bankwana da yunwa, rashin tsaro, da talauci.”
Wakar, wadda ta janyo cece-ku-ce dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari daga ranar daya ga watan Agusta, sakamakon tashin farashin abinci da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afrika.
Duk da yabon da Rarara ya ke wa gwamnatin, a kwanan nan sai da mahaifiyarsa ta yi kwanaki uku a hannun ‘yan bindiga, kafin daga baya suka sako ta.