Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sako Mahaifiyar Rarara


Mawaki Rarara da mahaifiyarsa
Mawaki Rarara da mahaifiyarsa

Bayan shafe kwananki 20 a hannun yan bindiga, Hajiya Hauwa’u Adamu mahaifiyar mawakin Najeriya Dauda Kahutu Rarara da aka fi sani da Rarara ta samu kubuta da saduwa da ‘danta.

Rarara ne ya sanar da haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Laraba da safe.

"Cikin yarda da amincin Ubangiji, mun samu dawowar Mama cikin aminci," in ji mawaƙin.

Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansan da ‘yan bindigan suka nemi a ba su kafin a saki mahaifiyar tasa.

'Yan bindigan da suka sace ta sun nemi a ba su Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG