Dan Najeriya Da Ya Zama Kyaftin Din Jirgin Yakin Ruwan Amurka

Ofishin Jakadancin Amurka Ya jinjinawa dan Najeriya Kelechi Ndukwe da ya kafa tarihi ranar na zama bakar fata na farko da ya jagoranci jirgin ruwan yakin Amurka.

Mayakin ruwan ya karbi jagorancin wani jirgin ruwan yakin Amurka mai suna USS HALSEY (DDG-97), wanda hakan ya sa ya zama Ba'amurke dan asalin Najeriya na farko da ya tara kai wa ga Wannan mukami.

Ya karbi shugabancin jirgin ne daga DeVere J. Crooks, wanda yake jan jirgin tun watan Nuwamba na shekarar 2019, a lokacin Ndukwe shi ne babba na biyu da ke biye da shi.

Mista Ndukwe, wanda ya kammala karatunsa a Jami’ar Notre Dame a 2002, ya kuma yi aiki a ofishin shugaban hadadden shugabannin hafsoshi (CJCS), babban jami’in soja na Amurka.

Yayin bikin mika aiki wanda aka shirya kai tsaye ta Facebook, Ndukwe ya tuno da yadda iyayensa suka yi kaura zuwa Amurka daga Najeriya a shekarar 1977 a matsayin "talakawan daliban kwaleji masu fata da buri." Ya kara da cewa a Amurka, komai na iya yiwuwa. ”

Ba wannan kara ne kada aka samun Amurkawa 'yan asalin Najeriya da ke samun daukaka a kasar, akwai ire-irensu da dam a fannonin kwon Lafita, wasannin da kuma nishadi.