‘Dan Iya Kan Makurden Kudaden Da Swiss Zata Dawowa Da Najeriya

FILE - A trader changes dollars with naira at a currency exchange store in Lagos, Feb. 12, 2015.

Kai jama’a lalle dai an cuci na ‘kauye inji ‘Dan Iya, saboda da gangan ake juya tunanin mu ya koma kamar na Tinkiya, muna ganin manyan kasar mu na ta faman nade mana dukiya, amma dayake sun ruga sunyi nasarar kashe mana zuciya, sai kagan mu cirko cirko mun zuba musu na mujiya.

Sai dai yanzu munayi wa Allah godiya, domin kuwa munyi sa’a wasu kasashen duniya sun amince su dawo mana da irin wannan dukiya gida Najeriya, alabarshi ‘yan kasa sa samu su wataya musammam ma dai idan sabuwar gwamnati tayi tsari na gaskiya.

Na Ikara yace ‘Dan Iya gaskiya naga kana ta wani fadi daga zuwa kusa da kai naga ka kama magana kana ta wani kaudi, amma yaya kake gani ya kamata ayi da wannan kudi? ‘Dan Iya yace eh to kaga dai tunda ance kudin nan sun kai dala miliyan ‘dari uku da saba’in, dole ne ‘yan kasa fa suyi zakwadi don kuwa da wannan kudi za’a iya kyautata rayuwar ‘yan kasa don kowa yaji dadi, zakuma a iya gina sabbin hanyoyi su shiga kurdi kurdi, hakanan za’a iya inganta wutar lantarki don muyi ta nishadi, sannan a tsarkake tsarin tsaron da yayi tsami ta hanyar shimfida sabon sharadi, kaga daga nan masu girgidi kan ‘dibar kudin kasar mu kuma sabon shugaba ya buga musu sabon gargadi.

Da sannu dai har Allah ya nuna mana karshen dukkanin karshen matsalolin da suka dame mu daga nan zuwa badi.

Saurari cikakkiyar hirar Na Ikara da ‘Dan Iya.