Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Dake Koyon Aikin Akanta Sunsha Alwashi


Kididdiga
Kididdiga

Sabon zababben shugaban dalibai a bangaren kidddiga wato (Accounting) a turance na kasa, Isah Yusuf Rimin Gado, a lokacin rantsar da su a jami'ar Bayaro da ke Kano, yayi kira ga matasa masu koyon karatun tsari da kiddidiga da su maida hankali wajen fahimtar karatun da kuma kokarin bada tasu gudunmawa a fannin kiddidiga.

Yayi nuni da cewar wannan kungiyar tasu ta kwashe sama da shekaru gomasha biyar bata tabuka wani rawar gani, amma a yanzu suna kokarin su ga sun samar da duk wasu abubuwa da suka kamata don tallafawa wannan fannin.

Babban abun da zasu maida hankali akai shine, suga sun samar ma dalibai damar da zasu yi amfani da kuma bada tasu gudunmawa a wasu dakunan karatu na yanar gizo da ake da su a duniya don kara bincike da kara yawan karatunsu, a kuma hannu daya kuma zasu ga sun bada matukar mahimanci wajen kyautata dangantakar su da wadannan kungiyoyin na kasa a bangaren kididdiga wato ICAN, ANAN don ba ma matasa karfin gwiwa a wajen neman ilimin kididdiga.

Shi kuma Farfesa Uba Adamu, na sashen koyar da aikin jarida a jami’ar Bayaro, ya kalubalanci sashen koyar da karatun kiddidiga da suyi kokarin kirkiro manhajar su ta koyar da ilimin akauntin daga tushe ba tare da sunyi amfani da na kasashen waje ba. Abu dayakamata suyi shine su samar da manhajar da akekira “Ethno Accountant” a turance, wato hanyar auratar da kididdigar ciniki a waje da ciniki a gida, wato ba kawai a cikin Najeriya ba harma da kasuwanin na kauyuka.

Yace idan akaje kasuwanin kauyuka za’aga suna mu’amala da kudi, amma babu takarda ko kwamfuta, to yakamata a samar da hanyar da za’a zamanantar da wannan hakara, don samun cigaba a fannin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG