Zauran matasa ya yada zango a babbar birnin tarayya Abuja, wanda wakiliyar mu Madina Dauda ta jagoran ta, sun kuma tattauna ne akan hanyoyin da za’a iya samu domin kawar da talauci ga matasan Najeriya.
Fatima dai tace Allah ne kadai zai iya yaye wa matasa talauci, amma da akwai hanyoyi da za’a iya yin amfani domin taka rawa wajen ganin an rage, idan matashi yana da hangen nesa kuma yasan yadda zai iya juya mayar da kwabo ya zama cici, rike kasuwanci da noma domin neman na kai da kawar da talauci.
Akwai matasa dayawa masu basira sun kuma iya sana’o’i amma babu jari, gwamnati zata iya taka rawar gani wajen tallafawa matasan da suke da basirar yin sana’a kowacce iri ce wanda basu da jarin da zasu iya bunkasa sana’ar tasu.
Duk da yake gwamnati bazata iya taimakawa dukkanin matasan Najeriya, don haka ya wajaba akan kungiyoyin matasa da matasa su tashi tsaye wajen ganin sunyi iyaka karfi.
Saurari muhawarar matasan.