Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Yasa Mata Basa Yawanta Fitowa Siyasa


Mai fafutukar Ilimin mata ta kasar Pakistan Malala Yousafzai,13 ga yuli, 2014.
Mai fafutukar Ilimin mata ta kasar Pakistan Malala Yousafzai,13 ga yuli, 2014.

Menene dalilin da yasa mata basa son fitowa a fafata dasu a al’amurran siyasa? Tambayar da mukayi wa lauya Aminu Hassan Gamawa na jami’ar Harvard, ya kuma bayyana mana amsar wannan tambaya.

Inda yace, mata na fitowa fagen siyasa matsalar dai itace siyasar da maza sukeyi an riga an gurbatar da ita, maimakon ayi abu cikin tsanaki cikin lumana sai a saka kwaya da ‘yan daba, wasu lokuta ba ayin taro a lokutan da suka kamata sai cikin dare wanda mata ba zasu iya zuwa ba.

Yanayin yadda ake gudanar da siyasa da kazantar dake cikin ta yasa wasu mata sun ja baya da abun, sai kuma maganar kudi dayawa duk mutumin da zai fito ya tsaya takara sai yana da kudin da zai rabawa jama’a, mata kuwa suna gidajen mazajen su basu da ire-iren kudade kamar haka.

Sai kuma yanayin tunanin jama’a kasancewa wasu na ganin ai siyasa abune na maza bana mata ba, wani lokaci kuma ana iya alakanta lamarin da addini, amma idan aka duba wasu kasashen musulmi da suka cigaba za’a ga cewa sun baiwa mata irin wannan damar batare da irin wadannan tunane tunane ba.

XS
SM
MD
LG