Dan Davido, Ifeanyi, Ya Rasu

Davido (Instagram/Davido)

A shekarar 2018, D’ Banj, ya rasa dansa Daniel mai shekara daya ta irin wannan hanya, inda shi ma ya fada tafkin ninkaya da ke gidan mawakin ya kuma rasa ransa.

Labarai a kafafen yada labarai a Najeriya na cewa Ifeanyi, da ga fitaccen mawakin Afrobeat Davido da suka haifa tare da budurwarsa Chioma Rowland ya rasu.

Ifeanyi, wanda shekarunsa uku kacal, ya rasa ransa ne a ranar Litinin, sanadiyyar nutsewa da ya yi a ruwan tafkin ninkaya kamar yadda fitaccen shafin Lindaikejiofficial, ya wallafa a dandalin Instagram.

Lamarin ya faru ne a gidan mawakin da ke unguwar masu hannu da shuni ta Banana Island a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya a cewar rahotannin kafafofin sada zumunta.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an garzaya da Ifeanyi asibitin Evercare da ke unguwar Lekki, inda daga baya likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Ku Duba Wannan Ma Reno Omokri Ya Tofa Albarkacin Bakinsa Kan Tara Wa Davido Kudi

Fitaccen shafin Instablog9na da ke bibiyan al’amuran fannin nishadi a Najeriya, ya ruwaito cewa, Ifeanyi ya kwashe tsawon lokaci a karkashin ruwan tafkin ninkayar, kafin daga bisani a ankara cewa ya nutse a ruwan.

Bayanai sun yi nuni da cewa an bar Ifeanyi ne a hannun masu renonsa a lokacin da lamarin ya faru kuma tuni an kama wasu daga cikinsu.

A cewar rahotanni, Davido ya tafi Ibadan domin halartar wani taron ahalinsa a lokacin da ibtila’in ya auku.

“Mutuwar da ba dadi, wannan labari ya girgiza ni matuka.” Jarumi A.Y. ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sai dai duk da wadannan bayanai da ke ta yawo a shafukan sada zumuntar, mawakin bai ce uffan ba.

Ku Duba Wannan Ma Ya kamata Mawaki Davido Yayi Taron Wake-wake Kyauta Ga Masoyansa - Tinubu

A makon da ya gabata, Ifeanyi ya cika shekara uku da haihuwa inda mahaifinsa ya wallafa hotonsa tare da taya shi murna.

“Za ka samu daukaka fiye da ni. Ina mai tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka dana.” Davido ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Idan har labarin ya tabbata, wannan lamari zai zamanto ba shi ne karo na farko da ya faru a tsakanin mawakan Najeriya ba.

A shekarar 2018, D’ Banj ya rasa dansa Daniel mai shekara daya ta irin wannan hanya, inda shi ma ya fada tafkin ninkaya da ke gidan mawakin ya kuma rasa ransa.