WASHINGTON, DC - Adeleke ya samu kuru’u 403,371, inda ya kayar da gwamna mai ci Adegboyega Isiaka Oyetola na jam’iyyar APC wanda ya samu kuru’u 375,027, yayin da Lasun Yusuf na jam’iyyar Labour (LP) ya samu kuru’u 2,729.
“A madadin shugaban hukumar zaben INEC mai zaman kanta, ina ayyana Ademola Adeleke Jackson Nurudeen a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun,” a cewar babban jami’in bayyana sakamakon zabe Farfesa Oluwatoyin Ogundipe na jami’ar Lagos.
‘Yan jihar Osun magoya bayan Adeleke sun bayyana farin cikinsu, wasunsu na cewa da ma ba wannan ne karon farko da Adeleke ya ci zabe ba in ba don an yi masa murdiya ba, sun kuma yaba wa hukumar zaben jihar kan kokarin da ta yi a zaben.
Magoya bayan sun kuma yi masa fatan alheri tare da yin kira a gare sa da ya yi aiki yadda ya kamata.
Saurari rahoton Hassan Umar Tambuwal: