Rashin samun wata amsa mai gamsarwa daga hukumar alhazzai ta COHO dangane da batun kudaden maniyata kimanin 158 da ba su sami zuwa kasa mai tsarki ba a yayin hajin 2022 ya sa kamfanin haji da umara na Sawki Voyage shigar da kara a gaban alkalin wata kotun birnin Yamai.
To sai dai hukumar alhazzai a ta bakin kakakinta Ali Saidou Zataou na alakanta rashin zuwan wadanan maniya kasar ta Saudiya da kurewar wa’adin dakon maniyata hasalima kamfanin na Sawki ya shigar da karar ne a wani lokacin da hukumar ke kokarin biyan wadanan maniyata 158 kudadensu cikin ruwan sanyi.
A dai dai lokacin da ake wannan dambarwa wasu kamfanonin na daban sun zargi hukumar ta alhazzai da danne kudaden dawainiyar wasu maniyata sama da 2000 wadanda suka hada masauki da abinci da kudaden inshora da bisa.
Da yake maida martani Alhaji Ali Saidou Zataou yace babu kamshin gaskiya a tare da wannan korafi.
A ranar 28 ga watan nan na satumba ne ya kamata lauyoyin kamfanin Sawki Voyage da na hukumar alhazai ta COHO su fafata a gaban alkali a kan makomar maniyata 158 da ake zargin sakacin hukumar ne ya hana masu safke farali a yayin hajin 2022.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5