Dalilin Rushewar Ginin Da Ya Kashe Mutum 2 A Abuja

Mahukuntan na duba wani gini da ya rushe a Abuja, Najeriya

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake zabga ruwan sama kama da bakin kwarya, kuma lamarin yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu yayain da aka zakulo wasu 37 da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba, a ginin mai hawa biyu da ya rushe a Unguwar Garki da ke Abuja.

ABUJA, NIGERIA - A daidai lokacin da ake cece-kuce kan kalaman sabon Ministan Kula da Birnin Tarraiyya Abuja Nyesome Wike na cewa zai rushe gine-ginen da ba su da cikakken aminci, sai ga shi wannan gini mai hawa biyu ya rushe har aka rasa rayukan mutane biyu.

Wani gini a Abuja, Najeriya da ya rushe ya kashe mutane biyu inda da dama suka makale

Wani dattijo da ya ce an haife shi a cikin Garki mai suna Alhaji Kasimu Mohammed, ya yi bayanin abin da ya sani akan gini yana cewa, tsohon gini ne wanda aka gina tun zamanin tsohon Shugaban kasa Sani Abacha saboda haka ginin ya dade sosai.

Kasimu ya ce ginin shaguna ne da ake da masu hayan shaguna kuma har suna kwana cikin shagunasu. Kasimu ya ce "mai gidan ya riga ya baiwa mazauna gidan wa'adi su tashi daga gidan, amma ba su riga sun tashi ba kafin wannan lamari ya faru."

Shi ma wani da ke makwabtaka da gini mai suna Haruna Aliyu Dass, ya yi karin haske kan abin da ya faru inda ya ce misalin karfe 11 na dare suna zaune kawai suka ji kara mai karfi na rushewar wani abu mai kaman gini, saboda haka sai ya bar inda yake zaune ya zo inda ginin ya rushe sai ya ga cewa ginin ya sauka kasa sosai har ya zama baraguzai.

Wani gini da ya rushe da mutane a Abuja, Najeriya

Haruna ya ce mutane biyu sun mutu nan take kuma an cire wasu mutane da dama har da ‘dan uwan sa wanda kansa ya fashe, an kai su asibiti.

Shi ma babban jami'in hukumar ba da agajin gaggawa na birnin tarayya Dr. Abbas Idris, ya yi bayanin irin kalubalen da ke tattare da irin wadannan gine-gine da ke rushewa akai-akai, inda ya koka da yadda mutane ba sa jin magana kuma basa tausayin talakawa, ga su da kwadayi da dabara, kuma suna da wayo.

Abbas ya ce mutane ba sa bin umurnin jami'ai masu kula da gine-gine saboda suna neman su sami kudi. Ya ce wannan gini an yi shi ne da farko a matsayin shaguna, kuma ginshikin ginin ba na bene ba ne, an yi ginin farko, an zo an dora wani akai, sai kuma a sake dora wani akai, sai ya zama gini mai hawa biyu wanda ba shi ne asalin irin ginin da ya kamata a yi a wurin ba.

Aikin Ceto mutane daga wani gini da ya rushe a Abuja, Najeriya

Abbas ya ce mutane biyu sun rasa ransu, amma an ciro wasu 37 da ransu, wasu kuma suna asibiti. Abbas ya kara da cewa za su ci gaba da tona baraguzan ginin ko za'a sami karin wasu wadanda ginin ya rufta da su a ciki.

A yanzu dai wannan shi ne gini na uku da ya rushe a cikin wattani biyu a birnin Abuja. An yi na farko a Gwarimpa, sai kuma aka samu wani a Deidei ga kuma wannan na Garki.

Mun yi kokarin samun bayani daga wurin masu kula da harkar gine-gine amma kokarin ya ci tura.

Saurari ciakken rahoto daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilin Da Ya Yi Sanadin Rushewar Ginin Da Ya Kashe Mutum Biyu A Abuja.mp3