Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gini Ya Rushe A Abuja Ya Kashe Akalla Mutane Biyu, Da Dama Sun Makale


Masu aikin ceto na tono mutane daga wani gini da ya rushe a Abuja, Najeriya
Masu aikin ceto na tono mutane daga wani gini da ya rushe a Abuja, Najeriya

Wani ginin bene mai hawa biyu ya ruguje a Abuja babban birnin Najeriya da yammacin jiya Laraba, inda akalla mutane biyu suka mutu, wasu kuma da dama suka makale.

WASHINGTON, D.C. - Wani shaidan kamfanin dilallancin labarai na Reuters ya ce ya ga gawarwaki biyu da aka ciro daga baraguzan ginin da ya rufta da misalin karfe 11:00 na dare (2200 GMT) a ranar Laraba. Mutane da dama kuma sun makale, sannan masu ba da agajin gaggawa suna ta kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Wani gini a Abuja, Najeriya da ya rushe ya kashe mutane biyu inda da dama suka makale
Wani gini a Abuja, Najeriya da ya rushe ya kashe mutane biyu inda da dama suka makale

Ginin ya kunshi gidajen zaman jama'a da kuma shagunan kasuwanci a cikin unguwar Garki da ke cikin kwaryar birnin Abuja.

Wani dan kasuwa daga wani gini da ke makwabtaka, Yakubu Inuwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Mun taimaka wajen fitar da wasu mutane, biyu da ba sa numfashi. An kuma fitar da mutane fiye da 20 daga cikin baraguzai."

Wani gini da ya rushe da mutane a Abuja, Najeriya
Wani gini da ya rushe da mutane a Abuja, Najeriya

Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, inda ba'a tabbatar da bin ka'idoji da kyau kuma kayan gini ba su da inganci.

📍 Muna tafe da cikakken rahoto mai karin bayani

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG