Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruftawar Gini: Cambodia Ta Tattabatar Da Mutuwar Mutum 26


Yanzu haka hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 26 tare da jikkata mutum 24, bayan da wani gini ya rufta da mutane da ke kwana a cikin ginin da ake ginawa a birnin Sihannoukville da ke gabar ruwa.

Akalla magina 26 aka tabbatar da mutuwarsu a Cambodia, bayan da wani gini da ake kan ginawa ya rufta a birnin Sihanoukville da ke gabar ruwa.

An kuma tabbata da cewa mutum 24 sun jikkata.

Yau Litinin masu ayyukan ceto sun ci gaba da tono baraguzan ginin ko akwai wadanda suke da rai.

Ma’aikatan na bacci ne a cikin ginin mai bene bakwai da safiyar ranar Asabar a lokacin da hadarin ya faru.

Amma wadanda aka ceto daga ginin sun ce akalla mutum 50 zuwa 60 ne suke amfani da ginin a matsayin wurin kwanansu.

Sai dai asalin benen ana gina shi ne a matsayin gidan haya wanda mallakin wani dan kasuwa ne a China.

A halin da ake ciki, ‘yan sanda na tsare da mutum 4, dukkansu ‘yan kasar China, domin yi masu tambayoyi, a kokarin da ake yi na gano musabbabin rushewar ginin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG