Dalilin Da Ya Sa PDP Ta Dakatar Da Ayu

Shugaban jam'iyyar PDP, Dr. Iyorchia Ayu

Dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC Hyacinth Alia ne ya lashe zaben gwamna a jihar Benue.

Reshen jam'iyyar PDP a jihar Benue da ke arewacin Najeriya ya dakatar da shugaban jam'iyyar Ayorchia Ayu bisa zargin sa da yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben da ya gabata.

A ranar 25 ga watan Najeriya ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, kana aka gudanar da na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 18 ga watan Maris.

Matakin dakatar da Ayu na zuwa ne bayan da PDP ta fadi a mazabarsa ta Igyorov da ke jihar Benue a arewacin Najeriya.

Dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC Hyacinth Alia ne ya lashe zaben gwamna a jihar Benue.

Yayin da yake karanta wata matsaya da jam’iyyar ta cimma, Sakataren jam’iyyar a mazabar ta Ayu, Vanger Dooyum, ya zarge shi da taka rawa wajen faduwar jam’iyyar a mazabar ta Igyorov da karamar hukumar.

Kazalika jam’iyyar ta ce Ayu bai yi zabe a ranar 18 ga watan Maris ba kuma mafi akasarin makusantansa jam’iyyar APC suka yi wa aiki a zaben.

Jam’iyyar har ila yau, ta zargi Ayu da kin biyan kudin da mambobi ke biya na shekara-shekara.

Kokarin jin ta bakin Ayu kan wadannan zarge-zarge.

Jam’iyyar ta PDP ta ce dakatar da shugaban nata ya fara aiki daga ranar 24 ga watan Maris.