Gidauniyar MEDICAID dake karkashin jagoranshin mai dakin gwamnar jihar Kebbi Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ita ce a sahun gaba wajen tattakin da ya sami halartar darurruwan mutane a babban birnin tarayya Abuja.
Tattakin dai ya hada mutane daga sassa daban-daban na Najeriya kuma a dau Shekaru 13 kenan ana gudanar da shi a kasar, ya zuwa yanzu mutane sama da dari uku ne suka ci moriyar tallafi karkashin gidauniyar.
A zantawar Dakta Zainab tare da wakiliyarmu a Abuja ta ce
cutar sankara tana da nau'o'i daban-daban, kuma gidauniyar na ba da tallafi ga ko wanne nau’i na cutar.
A shekarar 2020 kiddidiga ya nuna cewa a kasashe masu tasowa irin Najeriya a akalla mutane dubu 128 daga cikinsu mutane dubu 78 sun mutu.
Cutar sankara cuta ce da ke bukatar ingantattun na'urori na zamani don maganceta, da kuma magunguna sannan Cutar tana lakume makudan kudade a wajen magance ta kazalika ta tana halaka duban mutane a Najeriya dama duniya baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5