Dalilin Da Ya Sa Muka Rufe Asusun Ma’aikatun Gwamnati - Gwamnan Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir Yusuf)

Gwamna Kabir ya yi kira ga masu biyan haraji da su kwantar da hankalinsu yana mai ba su tabbacin cewa za a yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka kamata.

Gwamnan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin rufe daukacin asusun ma’aikatun jihar a ranar Laraba.

Yusuf ya ba da umarnin ne yayin wani taro da ya hada da shugaban hukumar harajin jihar da shugabannin ma’aikatun gwamnati a cewar rahotanni.

An ba akanta-janar na jihar umarnin da ya rufe daukacin asusun adana kudaden ma’aikatun a wani mataki na tabbatar da ana kashe su ta hanyar da ta dace.

Ana kuma sa ran bankuna za su mika takardun shaidar bin wannan umarni daga fadar gwamnatin don a tabbatar an rufe asusun.

Gwamna Kabir ya yi kira ga masu biyan haraji da su kwantar da hankalinsu yana mai ba su tabbacin cewa za a yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka kamata.