Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Sassauta Dokar Hana Fita A Kano


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnatin jihar Kano ta sake sassauta dokar hana fita a ciki da wajen birnin.

Rahotanni daga jihar sun ce yanzu an kara sassauta dokar inda za a rika fita daga 6 na safe zuwa shida na yamma.

A baya ana fita ne daga 8 na safe zuwa karfe 2 na yamma.

"Gwamnatin jihar Kano ta sake sa

A ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2024 gwamnatin jihar ta saka dokar hana fitar bayan da zanga-zangar kalubalantar tsadar rayuwa da ake yi a Najeriya ta jirkice ta koma tarzoma a jihar.

Wasu bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar suka yi ta fasa kayayyakin gwamnati da na ‘yan kasuwa, lamarin da ya hukumomin jihar suka saka dokar hana fita.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG