Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga Sun Kwashe Takardun Da Ake Tuhumar Ganduje Kan Rashawa A Kotu – Gwamnatin Kano


Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, (Hoto: Facebook/Abba Kabir Yusuf)
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, (Hoto: Facebook/Abba Kabir Yusuf)

Gwamnatin jihar Kano ta zargi masu zanga-zangar da suka far wa babbar kotun jihar da kwashe takardun da ake tuhumar tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan cin hanci da rashawa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin Gwamna Abba Kabir Yusu, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya kwatanta al’amarin a matsayin abin takaici.

“Babban abin takaici ne a ce makiyan jihar Kano sun dauko hayan wasu don su lalata daya daga cikin gine-ginen gwamnati masu dumbin tarihi da niyyar kawar da batun tuhumar da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da wasu daga cikin iyalansa da mukarrabansa.” In ji Tofa, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.

Gwamnatin Kano ta shigar da karar tuhumar tsohon Gwamna Ganduje da iyalansa da wasu mukarrabansa kan zargin karkata akalar dukiyar jihar ta Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kalaman gwamnatin ta Kano na zuwa ne bayan da Gwamna Yusuf ya kai ziyara harabar kotun a ranar Laraba don ganewa kansa yadda masu zanga-zangar suka lalata ginin kotun a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Ginin kotun na daga cikin wuraren da masu boren suka kai wa hari a ranar 1 ga watan Agusta, lamarin da ya kai gas aka dokar hana fita a duk fadin kwaryar birnin Kano.

Gwamna Yusuf ne ya gaji Ganduje a watan Mayun shekarar 2023 bayan da ya samu nasara a zaben da ya ba jam’iyyar NNPP nasara.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugaban jam’iyyar ta APC bai ce uffan ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG