Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Dokar Hana Fita a Kano


Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, (Hoto: Facebook/Abba Kabir Yusuf)
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, (Hoto: Facebook/Abba Kabir Yusuf)

Rahotanni daga jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an dage daukacin dokar hana fita a birnin da kewaye.

A ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2024 gwamnatin jihar ta saka dokar hana fitar bayan da zanga-zangar kalubalantar tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya ta jirkice ta koma tarzoma a jihar.

Wasu bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar suka yi ta fasa kayayyakin gwamnati da na ‘yan kasuwa, lamarin da ya hukumomin jihar suka saka dokar hana fita.

An samu rahotannin ‘yan sanda sun harbi wasu daga cikin mutanen da suka fito zanga-zangar ko da yake, ‘yan sandan sun musanta hakan.

Bayan da al’amura suka fara daidaita a mataki na farko, an rage dokar wacce daga 8 na safe zuwa 2 na yamma.

Sannan daga bayan sake rage wa daga 6 na safe zuwa shida na yamma.

A ranar Litinin hukumomi a jihar suka dage dokar baki daya, kamar yadda gidan rediyon Freedom FM ya ruwaito.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG