Wasu daga cikin muhimman abubuwa da aka cimma a yarjejeniyar da Gwamnati ta yi da kungiyoyin kwadago akwai karin Naira 35,000 ga duk ma'aikata har na tsawon watanni shida daga watan Satumba, da kafa wani kwamiti mai karfi cikin wata daya wanda zai duba batun karin albashi ga ma'aikatan kasar gaba daya.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Abdulaziz Abdulaziz ya ce Gwamnati za ta ba iyalai miliyan 15 kudi har Naira dubu 25,000 a wattani uku, daga watan nan na Oktoba zuwa Disamba na wannan shekarar, kuma karin albashi da aka yi har Naira dubu 35,000 zai kai ga tsofaffin ma'aikata da suka riga suka yi ritaya, wato masu karbar fansho. Haka kuma za a sayo motocin sufuri nan da watanni uku masu zuwa.
Abdulazizi ya kara da cewa za a janye harajin da aka sanya a harkar man gas wato Diesel na tsawon wattani shida daga wannan watan na Oktoba, za kuma a cire haraji ga wasu kamfanoni da daidaikun jama'a don saukaka masu wajen hada-hadar yau da kullum.
Shi kuwa Sakataren kungiyar TUC wanda shi ma ya rattaba hannu a cikin yarjeniyoyin, Kwamred Nuhu Toro, ya ce lallai kungiyoyin za su tabbatar cewa Gwamnati ta cika wadannan alkawuran da ta yi, saboda za su ci gaba da bibiya da sa ido, in ba haka ba kungiyoyi za su sake yunkurin shiga yajin aiki. Toro ya ce kungiyoyin ba za su janye yin taruka da Gwamnati ba har nan da wata daya domin su ga iya kokarin da Gwamnati za ta yi.
Amma mai nazari a al'amuran yau da kullum Dr. Abu Yazid, ya ce da alama wannan Gwamnatin za ta cika alkawari, amma kuma sai an yi hakuri .
Yazid ya ce kwamitin bincike da Gwamnati ta nada wanda ake kira The Investigator, ya riga ya samar wa Gwamnati kudade har Naira triliyan 10, saboda haka sai an yi hakuri za a samu nasara a wannan yunkuri.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da takardun da kotu ta sahale da su wajen amincewa da yarjeniyoyin fahimtar juna tsakanin kungiyoyin da Gwamnati cikin mako daya.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5