Yau kimanin kwanaki casa'in ke na da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban Chibok su fiye da dari biyu daga makarantarsu.
Rebeca Isaac 'yar shekaru 18 tana cikin wadanda suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram kuma ta je Abuja da 'yan uwanta hudu a suka samu tsira domin su gana da Malala.
Ta bayyana yadda ta kubuta. Tace basa cikin mota daya amma ita tun farko tace ba zata bisu ba. Ta gwammace da ta fita idan ma zata mutu ta mutu a tsinci gawarta ya fi mata. Ta fadawa adanda suke cikin mota tare ba'a mutuwa biyu. Haka tayi ta kubuta daga cikinsu.
Cikin wadanda suka raka 'yan matan zuwa Abuja akwai Mr. Shettima Haruna wanda yace yana da 'yarsa a hannun 'yan Boko Haram. Amma yace yana cike da kyakyawar fata dangane da dawowarsu gida. Yace gwamnati na kokari kuma kullum sun gaya masu za'a samo yaranasu. Yace da yadda Allah da taimakon mutane 'yan matan zasu dawo.
'Yan matan sun gana da Malala Yusufzai amma a asirce kuma ba'a gayyaci 'yan jaridun Najeriya ko daya saboda ita Malala an ce ta zo da 'yan jaridu 22. Amma Hadiza Bala Usman daya daga cikin masu fafitikar an sako 'yan Chibok din tace a idanunta Malala ta gana da 'yan matan.
Malala ta shahara akan ceto ilimin 'ya'ya mata sabili da haka zuwanta zai sa a kara karfi da karfe akan ilimin mata. Tun shekarar 2013 Malala ta kuduri aniyar ziyartar Najeriya sabili da a cewarta ilimin 'ya'ya mata na cikin hadari a Najeriya.
Daliban Chibok din da suka gana da Malala su fada mata ta gayawa shugaban kasar Najeriya ya dawo da daliban da aka sace, ya inganta tsaro a Chibok domin halin da suke ciki yanzu bashi da kyau. Sun bukaci yayi kokari kasarsu ta koma yadda take da lokacin da suke cikin zaman lafiya.
Ga rahoton Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5