'Yan tawayen sun fara ne da kai hare-haren bam da wasu motoci biyu da kuma wasu jerin hare-haren kunar bakin wake, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya mai hedikwata a Burtaniya.
'Yan tawayen sun kwace gine-gine da dama a unguwar Jobar, a wannan birnin mai cike da matakan tsaro, inda ke da tazarar kilomita biyu a arewa maso gabashin tsohuwar ganuwar birnin, inda har mazauna wurin ke cewa albarusan atilare da rokoki sun yi ta fadawa cikin tsakiyar birnin.
To amma, a cewar kungiyar rajin, bayan dannawar farko da 'yan tawayen su ka yi, sai jiragen yaki na gwamnati su ka yi da'ira a wuraren da 'yan tawayen su ka ja daga su ka yi masu luguden wuta har sau 30, wanda wannan ne al'amari na baya-bayan nan a wannan tashin hankalin da aka kwashe shekaru 6 ana yi.