Al’umomin yankin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kwace a jihar Adamawa, nata nuna farin cikinsu kan nasarar da dakarun sojin Najeriya da maharba harma da ‘yan Kato da Gora wato civilian JTF ke samu, wajen fatattakar ‘yan bindigar. Kamar ma yadda bayanai ke nunawa kawo yanzu an sami nasarar kwato garuruwa da dama dasuka hada da Gumbi, Meha dakuma wasu sassan garin Mubi.
Wasu mazauna yankin da ‘yan bindiga ke addaba, suna bayyana yadda mutane ke murna kan yadda ake kama ‘yan tada hankali tsaye kuma ana kashe su.
Ata bakin wani mutum daya nemi kar a bayyana sunansa, yace “hankalin mutane ya fara kwantawa a Mubi sosai yanzu, don saboda duk wadanda suke wasu garuruwa suna dawowa, kuma wasu dai an kona gidajen su, nagama motoci na lodi yanzu masu cin kasuwa na komawa, dama duk wanda gidajen su basu tabuba, ana dai samun nasara insha Allahu.”
Su kansu ‘yan sa kai na maharba da ‘yan Kato da Gora nama bayyana cewa yanzu hakama wasunsu sunyi nisa wajen kwato wasu sauran garuruwan dake hannun ‘yan Boko Haram, a don hakanema suka bukaci hukumomi dasu tallafa musu da kwararan makamai, baya ga abin masarufin da zasu ke barwa iyali.
Yanzu dai kungiyoyi dama sauran shugabanni nafa cigaba da yabawa tare kuma da kira kan a tashi a kare kai.
Your browser doesn’t support HTML5