A yanzu ‘yan kungiyar Boko Haram, na shan kashe, a hannun hadakan dakarun Sojojin Najeriya, da Maharba da kuma ‘yan civilian JTF, wato kato da gora, wanda hakan yayi sandiyar kwato wasu garuruwa, daga hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Garuruwan sun hada da Gombi, Hong da Maiha, yayi dama aka samu shiga wani yanki na Mubi, da ya sake fadawa hannan ‘yan bindiga, bayan da aka kwato shit un farko.
Alhaji Bako Ali Gwani, shugaban hadakan matasa, na ‘yan kato da gora wato civilian JTF, yace nasaran da ake samu ya biyo bayan hadin kai ne a tsakanin su da kuma daga jama’ar gari, ya kuma bukaci da jama’a, su ci gaba dayin adu’ar nasara.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa, NEMA mai kula da shiyyar Arewa maso gabas, Alhaji Muhammad Kanal, yace hukumar na yin duk abun da ya dace domin tabbatar da ganin cewa masu gudun hijiran sun samu tallafin da ya kamata.