A yau alhamis ne majalisar wakilan tarayya a Najeriya zata katse hutu domin ta zo ta nazarci rokon shugaba Goodluck Jonathan na kara tsawon wa'adin aiki da dokar-ta-baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Har yanzu dai Majalisar dattijan kasar ba ta amince da wannan bukata ba a saboda cijewar da wasu sanatoci suka yi cewa lallai sai dai a sake lale.
A yayin da ake hakan ne kuma, wata kungiyar matasa ta arewacin Najeriya ta yi gargadi game da illar yin hakan.
A halin da ake ciki, a yayin da mutane da dama suke dora laifin kasa shawo kan matsalar tsaron yankin arewa maso gabashin najeriya da ma wasu sassan a kan gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, wasu na ganin cewa laifin yana kan wasu shugabannin tsaro ne ‘yan arewa, wadanda aka damka wa hakkin tsaron kasa, amma basu yi ba, basu kuma ajiye aiki ba. Ali M. Ali shi ne babban editan jaridar Peoples Daily, kuma yana daya daga cikin masu irin wannan ra’ayin…