A ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, dakarun rundunar kawancen kasashen yankin Tafkin Tchadi ta hallaka wasu mayakan Boko Haram sama da 20.
Wata sanarwa da hedkwatar rundunar ta fitar wacce kakakinta Kanar Mohammed Dole ya fitar ta ce dakarun na MNJTF sun kuma ragargaza motoci biyar na yan ta'addan da aka girke masu manyan bindigigin harbo jiragen sama da ma sauran kayayyakinsu.
Shi da wannan farmaki mai take "Operation Saharan Fage" dakarun runduna ta uku dake monguno a Najeriya da runduna ta hudu a Diffa a bangaren Nijar su ne suka kaddamar da shi.
Da farko dai yan ta'addan sun nuna turjiya, amma biyo bayan barin wuta ba kakkautawa, dole ala tilas ba girma ba arziki suka saduda.
Dakarun na MNJTF sun kuma cafke mayakan na Boko Haram guda 17 a raye ko da yake, a nasu bangaren, dakarun sun yi hasarar jami'ansu guda shida.
A cewar masanin tsaro manjo Bashir Galma mai ritaya na mai cewa wannan nasara babban abin farin ciki ne don haka akwai bukatar kara kwazo da kuma yin amfani da bayanan sirri