An gwabza kazamin fada kusa da tashar saukar jiragen sama dake birnin Kunduz, lokacin da sojojin Afghanistan wadanda dakarun Amurka na sama suka rufawa baya, suka kaddamar da hari da niyyar sake kwato birnin daga hanun 'yan tawayen Taliban, wadanda suka kama garin dake arewacin kasar, tun ranar Lahadi.
Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid, da mazauna Kunduz sun gayawa Muryar Amurka cewa, an fara gwabza fadan ne a daren jiya Talata kusa da tashar jiragen saman ne, bayan da mayakan Taliban suka kaddamar da wani kazamin hari kan tashar jiragen saman, inda sojojin Afghanistan din suka fake ranar Litinin. Rahotanni sun ce wani gefen tashar yana hanun 'yan Taliban ahalin yanzu.
Jami'an gwamnatin kasar basu ce komi ba kan fadan da ake gwabzawa a baya bayan nan.
Tunda farko ma'aikatar tsaron kasar tace jami'an tsaronta ciki harda sojoji na musamman sun fara kai hare hare a wuren da mayakn Taliban din suke a safiya r jiya Talatan da zummar kutsawa cikin garin. Ma'aikatar tace jiragen yakin Amurka sun kai hari kan 'yan Taliban bayan ma'aikatar ta nemi taimakon su.