Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban Tace Ba-gudu-Ba-jada-Baya A Gwagwarmayar Da Take Yi


Mullah Akhtar Mansoor, sabon shugaban Taliban
Mullah Akhtar Mansoor, sabon shugaban Taliban

Sabon shugaban kungiyar Mullah Akhtar Mansoor ne ya bada wannan tabbaci

Kungiyar Taliban ta fidda wani sako cikin sauti daga sabon shugaban kungiyar Mullah Akhtar Mansooor, da nufin tabbtarwa shugabannin kungiyar, dattijanta, malamai da kuma almajirai cewa jihadin da kungiyar ta sa gaba zai dore har sai an shimnfida tsarin Islama a kasar Afghanistan.

Mullah Mansoor yace,dukkan shawarwari zasu dogara ne kan dokokin shari'a, kan aiwatar da yaki ne, ko gudanar da shawarwarin sulhu,daga nan ya shawarwari 'yan kungiyar su yi watsi da jita-jitar da ake yayatawa dangane da shirye shiryen kungiyar.

Sabon shugaban yace shugabannin kungiyar zasu yi bakin kokarinsu na tabbatar da hadin kai ta ko halin kaka. Yace marigayi Mullah Umar ya bashi dukkan aikace aikacen kungiyar tun yana da rai, sabo da haka yana ci gaba ne da aiwatar burin kungiyar bisa umarnin tsohon shugaban.

Dagewar da shugaba Mansoor yayi kan tabbatar da hadin kai tsakanin 'yayan kungiyar ya tabbatar da rahotannin da suka nuna cewa nadinsa ya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan kungiyar mai tada kayar baya.

Tunda farko yau Asabar kungiyar ta Taliban ta karyata rahotanin mutuwar Jalaluddin Haqqani, mutumin da ya kafa kungiyar Haqqani.

A jiya jumma'a kungiyar Taliban ta bada sanarwar cewa,an nada Sirajuddin Haqqani dan Haqqanin a zaman daya daga cikin na'iban Mullah Mansoor, sabon shugaban kungiyar Taliban.

Wata kungiya data balle daga Taliban da ake kira Fidai Mahaz, wacce ta fara tsegunta mutuwar Mullah, 'yan kwanaki da suka wuce, ta yi ikirari yau cewa, gaskiyar magana an kashe tsohon shugaban na Taliban Mullah Omar ta wajen bashi dafi.

XS
SM
MD
LG