Kungiyar Boko Haram na amfani da tashar wajen mayar da martani ga gwamnatocin da suke yakarsu, da kuma jan hankalin matasa wajen shiga ayyukan ta’addanci.
Kan wannan batu ne wakilin Muryar Amurka a Kamaru, Garba Awwal, ya nemi jin ta bakin shugaban matasa kuma dan kungiyar rajin kare hakkin bil Adama, Mallam Musa Usaini, wanda yace tabbas mutanen Kamaru sun zage dantse, domin ba zasu bari ba ayi amfani da wannan hanya wajen janyo hankalin mutane daga hanyar gaskiya zuwa hanyar ta’addanci ba.
Shima Haladu Gabdo, daya daga cikin masu bayar da shawara a hukumar harkokin cikin gidan Kamaru, ya ja hankalin jama’a da cewa duk wanda ya sani ko yaji labarin inda suke watsa shirye shiryen radiyon ya sanar da hukuma mafi kusa, kuma kada mutane suyi amfani da abinda suka ji daga wannan gidan radiyo.
Cikin kwanaki biyun da suka gaba ne maharan Boko Haram suka kashe wasu ‘yan kungiyar Kato da Gora biyu da wasu Makiyaya biyu, a gundumar Kwalfata.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5