A daya bangaren kuma, wani alkalin kotun tarayya a nan Amurka, ya ba gwamnatin shugaba Trump umurnin ta samar da kariya ga wasu bakin haure dubu 800,000 da suka shigo kasar nan tun suna kanana, wadanda aka fi sani da “Dreamers” a turance.
A wani mataki na shure matakin da shugaba Trump ya ke son ya dauka na kawo karshen shirin da ake kira DACA a takaice, wanda shi ya ba da dama bakin hauren suke zaune a Amurka ba tare da takardun iznin zama ba, Alkalin John Bates, ya kuma umurci hukumar tsaron cikin gidan Amurka ta Homeland Security, da ta karbi takardun sabbin masu son shigowa Amurka a karkashin wannan shiri, a karon farko tun bayan da aka samar da dokar a 2012.
Alkalin ya ce yunkurin da gwamnatin Trump ke yi na soke wannan shiri na DACA ya sabawa doka, amma a baya ya ba su kwanaki 90 da su gabatar da wata kwakkwarar hujja kan dalilinsu na so su soke shirin.
Amma har ya zuwa yanzu ba su gabatar da wata hujja ba.