Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da yadda jami’an hukumar farin kaya ta DSS ta kai wani samame gidan mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu da ke Kaduna a arewacin Najeriya.
Malam Mamu ne ya shiga tsakani wajen karbo kusan mutum 20 daga cikin fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a watan Maris.
Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ne daga Abuja a ranar 28 ga watan na Maris a lokacin da yan bindigar suka tsare shi har suka kashe mutum takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka, El Faruk Ahmed Mamu, kani ga Malam Mamu, ya ce da misalin karfe 12:30 dare aka kai samamen gidan yayansa.
“Jami’an SSS sun zo da motoci da dama da manya-manyan makamai, suka shiga suka yi bincike, duk da cewa ba su nuna wata takardar iznin bincike ba.
Ku Duba Wannan Ma Hukumar DSS Ta Tabbatar Da Kama Tukur Mamu Da Ya Shiga Tsakani Wajen Sako Fasinjan Jirgin Kasa Da Aka Sace“Cikin dare suka keta haddi da hakkin mata, suka shiga cikin gida suka rika bincike, duk wayoyin yaran gida suka kwakkwace.” In ji El Faruk.
Ya kuma kara da cewa sun debi takardu da kwamfutoci, yana mai cewa jami’an na DSS sun kuma kai samame ofishinsa sun gudanar da makamancin wannan bincike.
A ranar Laraba hukumar ta DSS ta kama Malam Mamu a filin tashin jirage na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Sun kama shi ne bayan da jami’an ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka tsare shi a kasar Masar suka maido da shi kasarsa bisa umarnin hukumomin tsaron Najeriya.
Malam Mamu na hanyarsa ta zuwa Umrah tare da iyalansa a lokacin da aka dakatar da shi a birnin Alkahira.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a a hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce ta kama Mamu ne don ya amsa wasu tambayoyi da ke da nasaba da tsaro.
Ku Duba Wannan Ma An Saki Karin Mutane Biyar A Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna"Muna masu sanar da cewa, abokanan huldar Najeriya a fannin tsaro na kasashen ketare, su suka kama Mamu a birnin Alkahira a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
"Daukan wannan mataki ya biyo bayan bukata da rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro da na tattara bayan sirri, suka mika ga abokanan hulda a kasar waje na a maido da shi zuwa Najeriya, don ya amsa wasu muhimman tambayoyi kan binciken da ake yi game da tsaro a wasu sassan kasa." Afunanya ya ce cikin sanarwar da Muryar Amurka ta samu kwafi.
A baya an taba zargin cewa Malam Mamu na da alaka da ‘yan bindigar da ke sace mutane, duba da rawar da yake takawa wajen hsiga tsakani, zargin da ya sha musantawa.
“Malam Tukur Mamu mutum ne na gari, wanda bisa radin kansa ya dauki ragamar shiga tsakani aka sako kusan mutum 20 daga cikin fasinjojin jirgin kasan nan da ‘yan bindiga suka kama.” Wata sanarwa da kamfanin jaridar Desert Herald ta wallafa sahfin yanar gizonta dauke da sa hannun shugaban ayyukan kamfanin Ibrahim Mada ta ce.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja domin jin abin da masana tsaro da masu kare hakkin bil adama ke cewa kan wannan lamari:
Your browser doesn’t support HTML5